Tuesday, 27 May 2014

Woozifa in Tijjani Doctrine


The walkway to the house of Sidina Shaykh Ahmad Tijani (ra).

It is here that the first wazifah and Dhikr Jumah was made before Shaykh Ahmad Tijani built his zawiyah. This long hallway is where wazifah was held and the original reason why Tijanis spread the white sheet for two reasons.

1. In Fiqh if a person isn't sure about the cleanliness of a place he should put a sheet down on the ground to cover and use that as a place of prostration.

2. The white sheet we learn in the Sharia was used by the Prophet on various occasions to honor some of his relatives when they visited as was the case when Dihab al Kalbi accepted Islam and also when a relative of his wife Khadijah (ra) visited him.

Tijanis lay the white sheet as a means of honoring the presence of the Prophet and his 4 companions that attend the wazifah after the 7th recitation of the Jawhara Kamal.

THE WAZIFAH consists of:

1.Take refuge in Allah

2.Al Fatiha ------------------------------------Once

3.Astagfirul Lahal `Azimal Ladzi Laa Ilaha Illa Huwal Hayyal Qayyum--------------(30

4.Salatul Fatihi--------------------------(50 times)

5.La Illaha Illallah---------------------(100 times)

6.Jawharatul Kamal---------------------(12 times)

Wazifah is the meeting of the brethren of the path to meet for the sake of Allah and to do audible zikr. The same adaab is given to the wird, wazifah, and zikr jumah as the adaab that is given in Salat. Meaning one must be in wudu, preferably in congregation, sitting in humbleness with proper sitting.
The Wazifah is done once ever 24hours at least. It can be done anytime but the preferred time is after Maqhrib.

It must be remembered that meeting for the sake of Allah is one of the ways of receiving shade under the thone of Arsh on the day when there will be no other shade as reported in the hadith:

Rasulullah Sallallaho alaihe wasallam has said that seven persons shall enjoy the shade of Allah's throne when there will be no other shade on the Day of Judgement:

(i) A just ruler

(ii) A young person who is nurtured in ‘Ibadat’ of Allah Ta’ala;

(iii) A person whose heart is attached to the Masjid;

(iv) Two persons who love each other for the pleasure of Allah; without any worldly motive, and they meet and separate in that spirit;

(v) A man who due to fear of Allah, refuses to go near a respectable beautiful woman, sexually inclined towards him, as also a woman who in a similar situation refuses to meet a man;

(vi) A person who gives Sadaqah so secretly that his left hand does not know what the right hand gives away;

(vii) A person who cries when remembering Allah in solitude.

Shaykh Ibrahim Niass (may Allah be pleased with him) said. "These are all difficult for the average person, but the easiest of them is loving and meeting for the sake of Allah."

This is one of the purposes of the wazifah, which is to meet for the sake of Allah. For the fuqara of this path, this is to be done everyday if one lives in a place where there are others who can meet.

Another fadl of the wazifa, is the recitaton of the Jawhara Kamal, which is another Sala al Nabi which was given to Shaykh Tijani as a gift from the Beloved Prophet (May Allah bless and give him peace).
The merits of this Sala ala Nabi follows.

As been described by the Grandest Muqaddam Sidi Ali Harrazem berrada al-Fasi and his successor in grandness Sidi Ahmed Skirej al-Fasi, the Jawhara is characterized by plenty of realities; (1) The Prophet, peace and blessing be upon him, and the Four Companions attend the circle of dhikr when it is recited more than 6 times, (2) One recitation of the Jawhara equals the prayers (tasbih) of the universe three times, (3) Gifting the Jawhara 12 times to the Prophet, peace and blessing be upon him, is like visiting him in his Rawda Sarifa, as well as all the other prophets and saints, (4) Gifting the Jawhara 7 times to the Prophet, peace and blessing be upon him, before sleep leads to seeing him in a dream (ruaya) (5) Reading the Jawhara daily results into the love of Sidna Mohammed, peace and blessing be upon him, to its reader

One must know of the secret of the Muhammadan Essence in the wazifa for even if you Hisb with the Abjad (numeric arabic table) the word

AL NABI

Alif- 1
Lam- 30

Nun-50
Ba-2
Ya-10

In the wazifah you will see this representation by the number of recitations of the zikrs in the wazifah.
The wazifah comprises of 30 Istighfirllah which is represented for the letter Lam in AL NABI. Lam = 30

Then there are 50 Salat al Fatihi, which is represented for the letter NUN
NUN=50

Then ther are 100 La Illah Illah ALlah which is 1 for Allah's Oneness. which is represented for the letter Alif

Then there are twelve Jawhartu Kamal, which is done 12 times, which is represented by the Ba (2) and the Ya (10).

The purpose of the Wazifah is to meet with your brothers in the religion for the sake of remembrance of Allah and his pleasure. And to be in the Presence of Allah's Messenger and His 4 Khalifas.

After this one makes supplication for the muslims, and families, and your own supplications. Then one departs with the Nafs awake ready for worship

Friday, 2 May 2014

Part 7

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin da ya Qagi halittar sammai da Qassai, sannan ya sanya duhu da haske acikinsu.Tsira da Aminci da Karimci da daraja su Qaru, su wanzu har abada abisa BABBAN BAWAN ALLAH, RAHAMAR ALLAH, FALALAR ALLAH, ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w) Da iyalan gidansa tsarkaka, da Sahabbansa madaukaka..Izuwa yanzu na tabbata duk mutumin da zuciyarsa take cike da imani ya gamsu da dukkanin hujjojin da muka yi magana akansu tun daga kashi na farko acikin wannan tattaunawa har izuwa kashi na 6.To amma duk da haka sai naga cewar ya kamata in sake kawowa ko da aya daya ne daga cikin Alqur'ani mai girma da kuma hadisi don Qarfafa dalili, kafin kuma in ci gaba da lissafa sunayen wasu daga Manyan Malaman duniya wadanda suka tafi akan wannan kyakkyawar fahimta ta yin taron maulidi domin girmama Annabi (s.a.w.w.).Acikin suratu Hud (a.s.) bayan Allah (s.w.t) ya gaya ma Manzonsa (s.a.w.w) labarurrukan Annabawan da suka gabace shi da kuma irin gwagwarmayar da sukayi da al-ummominsu, daga Qarshen surar sai yace masa:''kuma da yawa mukan Qissanta maka daga labarurrukan Manzanni (wadanda suka gabata). Gwargwadon yadda zamu tabbatar (zamu Qarfafa ) maka zuciyarka''. (sur. Hud, 119).Shehu Ibrahim Niasse (r.a) yake cewa ''in dai har Manzon Allah (s.a.w.w) zuciyarsa zata Qarfafa idan an bashi labarin Annabawan da suka gabata, to yaya kuma mu namu zuciyoyin ba zasu Qarfafa ba idan an karanta mana tarihin Manzon Allah (s.a.w.w).. (au kama Qalash Shaikh).To jama'a idan muka kalli wannan ayah da idon basira, ai ita kadai ma ta ishe mu hujjar taruwa ayi Maulidi.Jama'a Maulidin nan fa wallahi ayyukan alkhairi ne masu dimbin yawa akunshe acikinsa. Misali:a.) wa'azi da tunatarwa da nasihohi ta hanya jiyar da al-ummah tarihin Manzo (s.a.w.w) da yakokinsa da sauran gwagwarmayar da yasha fama da ita domin isar da saqon Ubangiji (S.W.T).b.) Karatun Alqur'ani da hadisan Manzo (s.a.w.w).c.) Rera yabon Manzon Allah (s.a.w.w) da iyalan gidansa Sahabbansa wadanda suka taimakeshi wajen isar da sakon Ubangiji (s.w.t.).d.) zikirin Allah da salati ga SHUGABA (s.a.w.w).e.) shigar da soyayyarsa da Qaunarsa cikin zukatan manya da Qanqana, ta hanyar fa'dar siffofinsa da halayensa, da mu'ujizozinsa (s.a.w.w).f.) taimakawa juna cikin bin Allah, ta hanyar zumunci da kuma haduwa da juna abisa manufa guda. Wato girmama Manzon Allah (s.a.w.w).g.) ciyarwa da shayarwa fi-sabilillahi.To 'Yan uwa idan kuka dubi wadannan abubuwan da na lissafta a sama da ma wasunsu wadanda na manta ban fa'da ba, ai zaku ga cewar dukanninsu ayyukan alkhairi ne wadanda musulunci yake umurni dasu.Da wannan nake Qara ba ma 'Yan uwana shawarar cewa lallai ne mu kawar da kanmu daga maganganun maqiya, kuma muci gaba da girmama Manzon Allah (s.a.w.w) da kuma duk wani mutum ko wani abu wanda yake da nasaba dashi (s.a.w.w).Domin kuwa Manzo (s.a.w.w) ya bamu labarin cewar adaren da akayi Isra'i da Mi'iraji da shi, lokacin da suka iso wani gari wato ''Baitul laham'' (bethlehem) sai Mala'ika Jibrilu (a.s) ya umurce shi da cewar ya sauko yayi sallah raka'a biyu.Bayan ya idar sai Mala'ikan ya tambayeshi ''YA MUHAMMADU ka san ko awanne waje ne kayi sallah?''Sai yace masa ''A'a''Sai yace ''ai kayi sallah ne awajen da aka haifi Annabi Eesa (a.s).To anan zamu iya fahimtar cewa ashe guraren da aka haifi Annabawa (a.s) suna daga cikin 'Sha'a'irul Lah'.(alamomi, ko kuma guraren girmamawa na Allah). Ba don haka ba, da Mala'ika Jibreelu (as) ba zai umurci Manzon Allah (saww) cewar yayi sallah awajen ba.* In dai har guraren da aka haifi Annabawa yana da muhimmanci acikin addini, to yaya kuma RANAKUN HAIHUWAR, DA KUMA WADANDA SUKA HAIFESUN??Don karin bayani Aduba sunanun Nasa'i, juzu'i na 1, shafi na 241, hadith mai lamba 448).Ya Allah ka Qara cika zuciyoyinmu da tsantsar Qaunar Manzon Allah (s.a.w.w) da kuma Girmama shi tare da dukkan abinda ya rataya dashi.Masu tada jijiyar wuya, suna kumfar baki har suna Kafirta Muminai Masoyan Manzon Allah (saww) saboda suna yin Maulidi, ko kuma awasu lokutan sai kaji suna kiran mutane da sunannaki Kala-Kala.Ko suce maka Dan-bidi'ah, Ko suce maka mushriki, duk dai saboda kana Girmama Manzon Allah (saww) ta hanyar da su ba'a koyar dasu ba.Ko ba'a yiwa mutum bayani ba, yasan cewar Wadannan kalmomin da makamantansu, basu acikin koyarwar Islama.Shi taron Maulidi mu mun dauke shi amatsayin wata sunnah ce mai kyau daga cikin sunnonin Musulunci.Domin kuwa tun farkon musulunci akwai irin wadannan ayyukan. Kuma Manzon Allah (saww) yana cewa:"DUK WANDA YA SUNNANTA WATA SUNNAH MAI KYAU ACIKIN MUSULUNCI, TO YANA DA LADANTA DA KUMA KWATANKWACIN LADAN WADANDA SUKAYI AIKI DA ITA. BA ZA'A TAUYE KOMAI DAGA LADANSU BA. HAR ZUWA TASHIN ALQIYAMAH. KUMA DUK WANDA YA SUNNANTA WATA MUMMUNAR SUNNAH ACIKIN MUSULUNCI, TO YANA DA ZUNUBINTA DA KUMA KWATANKWACIN ZUNUBIN DUK WANDA YAYI AIKI DA ITA HAR IZUWA TASHIN ALQIYAMAH.BA ZA'A TAUYE KOMAI BA DAGA CIKIN ZUNUBINSU"(aduba Sahihu Muslim, hadisi na 1017).Idan muka dubi irin kyawawan ayyukan da suke kunshe acikin wannan al'amarin na TARON MAULIDI, mu da kanmu mun san cewar Taron Maulidi yana daga cikin "SUNNATUN HASANATUN" din da ake nufi.Sannan adaya gefen idan muka dubi muka dubi yadda wasu suke kafirta 'yan uwansu musulmi tare da zaginsu da bakaken maganganu, don kawai sabanin fahimta, da kuma yadda suke raba kan al'ummar Annabi (saww) tabbas ko shakkah babu mun san inda zamu ajiye su shine.. "SUNNATAN SAYYI'ATAN".Da fatan Allah ya kiyaye mana imaninmu.Insha Allahu akashi na takwas zan kawo mana misalai daga cikin ayyukan magabata.

Part 6

Tsira da Amincin Allah da daukaka da daraja da martaba su Qara tabbata ga MATATTARAR BAIWA, ALFAHARIN BANU HASHIM, ANNABI MUHAMMADU da iyalan gidansa tsarkaka da sahabbansa mahaskaka..Bayan haka ina Qara jawo hankalin duk wani masoyin Annabi (s.a.w.w) da cewar Mu dage mu jajirce muyita hidima domin nuna murnar mu dangane da tunawa da haihuwar FIYAYYEN MANZANNI (s.a.w.w).Domin kuwa yin haka ibadah ce wacce take matukar Qara kusantar da bawa izuwa rahamar Mahaliccinsa. Kuma ana amfana da ita: Ko da kuwa wanda ba Musulmi ba idan yayi murna da zuwan Annabi Muhammadu (saww) to Wallahi zai amfana.Imamul Bukhariy ya ruwaito hadisi daga 'Urwatu (r.t.a) cewa: ''Thuwaibah baiwar Abu-lahab ce wacce ya 'Yanta ta (saboda murna alokacin da ta bashi labarin haihuwar Annabi s.a.w.w) sannan kuma daga baya ta shayar da Manzon Allah (s.a.w.w).Bayan Abu-lahab ya mutu, sai wani (Sahabi mumini) daga cikin danginsa ya ganshi amafarki acikin mummunan yanayi. Sai ya tambaye shi.. ''Ya aba_lahab, me ka riska?''Sai yace ''Wallahi tunda na rabu daku ban samu wani hutu ba. Sai dai kawai ana shayar dani ruwa (mai dadi) ta tsakanin babban yatsana da sauran yatsu, saboda dalilin 'Yantar da Tsuwaibah da nayi''(aduba Sahihul Bukhariy Juzu'i na 7, hadisi na 38 acikin Kitabun-nikahi).To Jama'a wannan fa kafiri ne, kuma babban makiyin Annabi (s.a.w.w) amma gashi ya amfana ta dalilin yayi murna da haihuwa Annabi (s.a.w.w).. To yaya kuma Musulmi Mumini sadiqi idan ya tara jama'a ya ciyar dasu ya shayar dasu don nuna Qauna da murnarsa saboda zuwan Manzon Rahama (s.a.w.w)!!Kuma Karku manta cewar shi fa Abu-Lahab alokacin da ya nuna wannan murnar, yayi ne domin zumunci. Ba wai don girmama Annabin ba.Domin kuwa alokacin bai san WANNAN JARIRIN SHINE ANNABIN QARSHE BA, BAI SAN CEWAR WANNAN JARIRIN SHINE MAFI DARAJAR HALITTAR ALLAH BA. (saww).Kuma ku dubi irin amfanuwar da ya samu ta dalilin wannan murnar da yayi sau daya.. Duk da cewar daga baya ya zamto Qaton kafiri, mafi chutarwa ga Annabi (saww).Sannan wata isharar da zamu sake daukowa akan Halaccin Taron Maulidi daga Hadisan Annabi (saww) shine: A lokacin da SHUGABA (s.a.w.w.) yazo madina ya samu Yahudawa suna azumi tare da bukunkuna. Sai ya tambaya saboda menene?Sai aka ce masa ''SUNA YI NE SABODA TUNAWA DA RANAR DA ALLAH YA TSERATAR DA ANNABI MUSA (AS) DAGA SHARRIN FIR'AUNA"Sai Annabi (s.a.w.w) yace ''AI MU MUKA FISU CHANCHANTA DA ANNABI MUSA.''Saboda haka ya umurci musulmai suma su rika yi..(aduba Sahihu Muslim, juzu'i na 2, shafi na 147, hadithi mai lamba 1130).Abin lura acikin wannan hadisin shine:a.) Annabi (s.a.w.w) ya yarda da yin wata ibada ta musamman domin tunawa da wani abu muhimmi na tarihi.b.) Musulunci yana karbar abu mai kyau wanda babu sa'bon Allah acikinsa. Ko da kuwa daga gun yahudawa ne.c.) In dai har Annabi (s.a.w.w) ya yarda agirmama ranar da Allah ya tseratar da Banu Isra'eela daga zaluncin fir'auna, to ashe kenan muma ya kamata, ya kuma dache mu girmama ranar da Allah ya kawo mana RAHAMARSA wanda ya tseratar da DUKKAN duniya daga duhun kafirci da jahilci da zalunci.. wato Annabi Muhammadu (s.a.w.w).Na san zaku yimin tambayar da kuka saba yimin.. cewar to me yasa Sahabbai (r.t.a) su basuyi ba??To ni kuma sai in baku amsa daki-daki kamar haka:a.) kasancewar Annabi (s.a.w.w) be yi abu ba, Sahabbansa basuyi ba, BA HUJJAH BANE cewar na bayansu ba zasu yi ba.!!.Hujjah ita ce kace mana ANNABI YA HANA..Kamar yadda na fa'da a chan bayan (part 3),Ya kamata kusan cewar asalin kowanne abu halal ne acikin addini. Saidai kadai wanda shari'a ta hana. Ta hanyar aya ko hadith ingantacce..B.) Imamu Ahmad ya ruwaito hadithi daga Ibn Mas'udin cewar ''Duk abinda Musulmi suka hadu akan cewar yana da kyau, to agun Allah ma mai kyawu ne..''Kunga kuma duk musulmin duniya sun yarda da cewa MAULIDI ABU NE MAI KYAU.In banda wahabiyawa babu wani wanda yake jayayya akan wannan..Su ma muna yi musu fatan Allah ya ganar dasu..C.) duk wani abu mai kyawu wanda yake akwai wata maslaha ta addini acikinsa, to yinsa halal ne..Idan kuwa muka duba da idon basira zamu ga akwai Masalihu Masu yawa acikin Taron Maulidi wanda al'ummar Musulmi Suke yi ayau.Misali:1. Halartar guraren Maulidi yakan Qara wa Mutum Jin nauyi da kuma ganin girman Annabi (saww). Saboda Zurfafan Maganganu da zaka ji acikin tarihinsa (saww) wadanda idan littafi zaka Sanya agaban Malami, to sai kayi shekara da shekaru iliminka bai kai gun ba. Amma Idan ka halarci wajen Maulidi sai kaji ana ta fadarsu.2. Halartar wajen Maulidi yana Qara chusa wa Qananan Yaranmu Son Annabi (saww). Ta yadda zaka ji yaro Qanqani ya iya rera Qasidun Yabon Ma'aikin Allah (saww).Yin hakan kuwa ya dache da bin umurnin Annabi (saww) acikin Mash-hurin Hadisin nan: "ADDIBU AULADAKU"3. Halartar Guraren Maulidi yakan bada wata muhimmiyar dama ga Al'umar Musulmi domin sada zumuncin da yake tsakaninsu, da Kuma samun lada ta hanyar ciyarwa da shayarwa da kuma Wa'azantar da Juna.D. A Musulunci akwai abinda ake kira "AS-SUNNATUL-HASANAH". Maulidi yana daga cikin wannan jerin abubuwan

Part 5

ALHAMDULILLAHI mun gode ma Allah wanda ya sanya mu acikin kebantattun wannan al'ummah wajen nuna murnarmu da biyayya da girmamawa abisa Janibin SHUGABA (s.a.w.w).Awancan sati da ya gabata, na kawo wasu daga cikin ayoyin Alqur'ani mai girma wadanda suke ishara izuwa halascin yin taro domin murna da farin-ciki da samun Manzon Allah (S.A.W.W). Kuma na kawo fassarorin da Manyan malamai masanan tafsiri suka yima ayoyin.Kamar yadda Shaikh Muhammadul Alawiy Almalikiy yake cewa ''mu ba wai muna magana ne akan halascin yin mauludi sau daya, ko wata daya ashekara kawai ba, A'A. mu muna magana ne tare da kafa hujjoji akan WAJIBCIN tuna shi da kuma yin mauludinsa ako yaushe ako wacce rana''.''Sai dai dole ne ya zamto murnar mu da karsashin mu ta fi yawaita acikin watan Rabi'ul Awwal, domin shine watan da aka haifa mana wannan BABBAN MASOYI (s.a.w.w)'Yan uwa ku sani cewar yin murna da girmama wata rana ko wani lokaci kebantacce saboda dalilin wata kebantacciyar baiwa wacce Allah yayi maka, wannan ba bid'ah bane. Ba kuma sabon abu bane acikin addini.Domin kuwa yazo acikin Sahihul Bukhariy da Sahihu Muslim a Kitabul fadha'il, da kitabu salatil jumu'ah, da kitabur- riqaaq, wajen da Manzon Allah(s.a.w.w) yake fadar falalar ranar Jumu'ah. Yana cewa ''acikinta ne aka halicci Annabi Adam, kuma acikinta ne aka karbe rayinsa..''Kunga kenan ashe wannan yana daga cikin dalilan da yasa ranar jumu'a ta zama ranar Eedi ga Musulman wannan Al'ummah..Kuma an ruwaito cewar Shi kansa (s.a.w.w.) ya kasance yana girmama RANAR DA AKA HAIFE SHI.Domin kuwa Abu-Qatadah Al-ansariy (r.a) ya ruwaito cewar an tambayi SHUGABA (s.a.w.w) dangane da azumin da yake yi duk ranar litinin. Sai yace:''ita ce RANAR DA AKA HAIFENI, kuma ita ce ranar da aka fara saukar min da wahayi''(aduba Sahihu Muslim, hadith mai lamba 2606, da kuma SUNANUL KUBRA na Imamul Baihaqiy, juzu'i na 4, shafi na 300, hadith mai lamba 8182, Da kuma mai lamba 8259.. Imamu Ahmad, da Imam An-Nasa'i duka sun ruwaito kuma sun inganta hadithin)Ga hujjah nan ta bayyana Qarara cewar Manzon Allah (s.a.w.w) yana yin azumin ne domin nuna godiyarsa ga Allah (SWT) abisa ni'imar bayyanar dashi aduniya, da kuma ni'imar sanya shi acikin Manzanni (a.s.). Shi yasa yake yin wannan ibadah ta Musamman.To saboda haka ya halasta mutum yayi ado, ya tara jama'a, ya chiyar ya shayar domin MURNA da kuma GODIYA ga Allah (swt) abisa ni'ima da baiwar da yayi mana da ya bamu MANZON ALLAH (s.a.w.w). saboda shima ciyarwar da shayarwar, duk fannin ibada ne..Saboda haka duk mai cewa 'ai Annabi be yi Maulidi ba' to Qarya ne.. Annabi yayi.. Domin kuma ba wani abu bane maulidin illa nuna murna da kuma godiya ga Allah abisa wata ni'imar da yayi..Saboda Maluman Usulul-Fiqhi sunce ana cirowa Hukunci ne ta hanyoyi biyar kamar haka:1. ZAHIRIN NASSI.2. ISHARA DAGA NASSI.3. DILALAR DA NASSIN YA SHIRYAR.4. ABINDA NASSIN BA YA CIKA SAI DASHI.5. KO KUMA MAFHUMUL-MUKHALAFAH.Masu Qin Mauludi suna tambaya ta cewar ''toh munji ka kafa hujja da dalilai masu Qarfi akan halarcin taruwa ayi Maulidi. To me yasa sahabbai basu yi ba?''Na baku amsa a (part 3) amma naga kamar har yanzu baku gamsu ba, to ku jira fitowar (part 6) INSHA ALLAHU Zan ci gaba daga inda na tsaya.Ya Rasullahi ka yarda da soyayyar da muke yi maka don albarkacin Nana Fatimah (a.s.) ameen.

Part 4

A ci-gaba da Muke yi wajen Tsamowa Nassosi daga Ayoyin Al-Qur'ani mai girma wadanda suke yin ishara izuwa Halarcin taruwa ayi Murna da Zuwan Annabin Rahama (saww), Wannan Karon muna so 'yan uwa suyi duba da idon basira izuwa wasu ayoyi guda biyu masu kama da juna wadanda kuma dalilin saukarsu ya zamto kusan iri daya.Wannan Ayar tazo ne afarko-farkon Suratul-Jumu'ah, Bayan Allah (swt) Ya gayawa Muminai ni'imar da yayi musu ta dalilin Aikowar Annabi (saww), sai kuma yace:''Wannan falalar Allah ce, yana bayar dashi ga wanda yaso. Kuma Allah Ma'abocin falalah mai girma ne'' - (Suratul Jumu'ah Aya ta 4; da kuma suratul hadeed aya ta 28)Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (r.t.a) ya fassara wannan aya ta sama da cewa:Ma'anar ''Allah ma'abocin falala mai girma ne'' shine saboda MUSULUNCI da kuma ANNABTAR da ya bayar ga ANNABI MUHAMMAD (s.a.w.w.).Awani Qaulin kuma aka ce ma'anar 'Falala mai girma' ita ce musulunci.Awani Qaulin kuma aka ce 'MANZON ALLAH (s.a.w.w) da kuma ALQUR'ANI MAI GIRMA, sune wannan falala da ake nufi.(aduba ''TANWEERUL MIQBAAS MIN TAFSEERI IBN ABBAAS don Qarin bayani)To 'yan uwa, abin lura acikin fassarar wannan aya shine: ita ma tana tabbatar mana da cewa ANNABINMU (s.a.w.w) shine FADHLUL-LAHI (falalar Allah)..To ashe shi ake nufi da cewar MUYI MURNA saboda shi.. (acikin ayar 58 ta suratu Yunus a.s).Idan kuma mutum ya dage akan cewar "FADHLUL-LAHI" tana nufin Musulunci ne ko kuma Alqur'ani Mai girma, ba Annabi (saww) ba, To Sai mu tambaye shi:TA DALILIN WANENE AKA SAMU MUSULUNCIN DA KUMA AL-QUR'ANIN???Amsar dai guda daya ce- "MAULANA MUHAMMADUR-RASULULLAH (SAWW)"* Hujjah ta tagaba tana cikin suratu Maryam (a.s), dangane da tarihin Annabi Yahya (a.s). Allah (s.w.t) yana ce mana: ''KUMA AMINCIN ALLAH YA TABBATA AGARESHI ARANAR HAIHUWARSA, DA RANAR MUTUWARSA DA KUMA RANAR DA ZA'A TASHESHI YANA RAYAYYE'' (sur. 19, aya ta 15).Wannan ayar tana ishara agaremu cewar RANAR HAIHUWAR ANNABAWA (a.s.) ashe RANAR AMINCI CE ga shi kansa Annabin da kuma al'ummar da aka aikoshi cikinsu..Kuma Allah bai hana muyi murna da muhimman ranaiku acikin rayuwarmu da addininmu ba.Awani Wajen Kuma Allah (s.w.t) yake cewa: ''Hakika mun aiki Annabi Musa da ayoyinmu (da kuma umurnin) cewar ''Ka fitar da mutanenka daga duhun (kafirci) izuwa haske.. Kuma ka tunasar dasu Dangane da RANAKUN ALLAH'' (aĆ½yamil Lah)- suratu Ibraheem (a.s) sur. 14 aya ta 5.* Menene Ma'anar kalmar 'RANAKU ko kuma KWANUKAN ALLAH'??Al-Imamul Baihaqiy ya ruwaito acikin littafinsa 'SHU'ABUL IMAN' cewar: "Ma'anar KWANUKAN ALLAH shine albarkokinsa da kuma ayoyinsa.To idan kuwa haka ne, to wacce FALALA CE, wacce NI'IMA CE, wacce ALBARKA CE ta kai kamar samun ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w)???Don Allah Ku bani amsa.

Part 3

Tun lokacin da na fara rubutu akan Mauludin Annabi (s.a.w.w) na hadu da chalenges kala-kala daga maqiyan al'amarin.Wadansu sukan zageni (ta inbox), wasu kuma sukanyi comment a wall dina, suyi ta jayayya da musu akan cewa su basu gamsu da hujjojin ba. Duk da cewa har yanzun ban fadi wani ra'ayi nawa ba, illa dai abubuwan da manyan Maluma suka rubuta a litattafansu.. Kuma dukkansu sukan ciro hujjojinsu ne daga ayoyin Alqur'ani Mai tsarki, tare da tafsirin ayoyin ta hanyar ruwayoyi ingantattu daga manyan Sahabbai.. Amma duk da haka, makiyan Mauludi sai Qara kumfar baki sukeyi.Kasancewar duk hujjojin da nake kawowa sunfi Qarfin turuwa ta kowacce hanya, (tunda ayoyi ne ba hadisai ba. Ballantana mutum yace hadisan basu inganta ba..)Sai suke tambaya ta wai''shin, Sayyiduna Abubakar da Umar da Uthman da Aliyyu (r.t.a) dasu Imamu Malik dss, me yasa su basu yi Mauludi ba? Ko kuwa su basu fahimci wadannan hujjojin naka bane?''To amsa ta ga masu irin wannan tambaya ita ce:1. Asalin kowanne abu a addini, HALAL ne. Komai da Komai. Sai illa abubuwan da shari'a ta haramta.. Ta hanyar ayar Alqur'ani, ko hadisi ingattatce..Sannan kuma addini bai bada damar ka hana wani mutum yin wani abu wanda aka samu sabanin Malamai akansa ba..Saboda haka masu kin Mauludi, idan kuna so mu hanu mu dena, sai dai ku kawo mana hujjar da ta hana yin Mauludi.. Daga Alqur'ani ko hadisi, ko ijma'i..Na san cewar kuna yawan kafa hujja da ''Fa inna kulla muhdathatin bid'ah, wa kulla bid'atin dhalaalah''..To ya kamata kusan cewar wannan kalmar ''KULLU'' din tana zuwa da ma'anoni da yawa a larabci. Tazo awurare da dama amma kuma da ma'anoni mabambanta.Idan kunce Ai Maulidi bidi'a ne,to mu kuma sai mu Qara tunatar daku cewar* Musabaqah ma Bidi'a ce.* Kafa Qungiya ma Bidi'a ne.* Ware Masallaci ma (saboda bambancin Ra'ayi) Bidi'a ce Muharramah.* Sanyawa Masallatai ko Makarantu sunayen Sahabbai ma Bidi'ah ne.* Bikin yaye Dalibai ma Bidi'a ne.Tambaya anan ita ce: Me yasa duk wadannan Bidi'o'in baku yin inkarinsu???Maimakon haka ma sai ku ka daukesu kuke aikatawa Kullum, ku ka Maishe su Sunnoninku???Har ya zamto Mabiyanku basu iya bambancewa Tsakanin Sunnonin Annabin Rahama (saww) a kuma Sunnoninku na Son Zuciya???Me yasa Ranku ba ya baci sai kunga ana Murnar Haihuwar Manzon Allah (saww) ???Anya Wannan ba alamar Munafurci bane???Hatta ita Qasar da take bunkasa wannan Aqeedar Munafurcin aduniya, Ta yarda kuma ta Amince wa Kiristocin Sojojin Amurka da suke girke akasar cewar Su gudanar da Bikin Kirsimati. Amma bata yarda Maluman Sufaye na Qasar Su Gudanar da taron Maulidin Manzon Allah (saww) ba!!!* Sannan dukkan Sarakunan Ita Saudiyyar da Ameerai maza da mata su kan gudanar da Bukukuwan Birthday nasu idan ranar haihuwarsu ta kewayo. Amma me yasa maluman Qasar basu yin inkari??Anya Wannan ba yana Nuna Tsantsar Qiyayya ga Manzon Allah bane acikin zukatansu, alhali abaki suna nuna cewar su mabiya sunnah ne??Ya kamata dai masu kushe harkar Maulidi su fahimci cewar: idan ma an tafi akan cewa bidi'ah ne, to ai bidi'ar ta kasu kashi-kashi.1. Akwai bid'ah muharramah,2. akwai bid'ah wajiba,3. akwai bidi'ah Mandubah,4. akwai bid'ah makruhiyah,5. akwai bidi'a mubahiyah.Don Qarin bayani aje aduba littafin 'IH-YA'US_SUNNA H' na Shaikh Uthman bn Fudiy (r.t.a).Anan za'a ga Matsayin Maulidi.Da fatan wadannan hujjoji nawa zasu gamsar da duk wani mai neman gaskiya..YA Allah KA Qara ganar damu. Allah KA Qara mana SON ANNABI (s.a.w.w).. Ka bamu dukiya mai yawa wacce zamuyi ta hidima da ita abisa JANIBIN SHUGABANMU (s.a.w.w).

Part 2

Abinda zamu fara kafa hujja dashi, shine ayoyin Alqur'ani Mai Girma.Ayah ta farko za'a sameta acikin Suratu Yunus (a.s) surah ta 10 ya ta 58, Wajen da Allah (SWT) yake cewa: ''(YA MUHAMMADU) kace musu -da falalar Allah ne da kuma rahamarsa. Da wannan ya kamata suyi farinciki.. Domin shine mafi alkhairi daga (arzikin) da suke tarawa''.Toh gashi dai ayah tayi bayani Qarara, sai dai kash! Wadansu mutanen sun kasa fahimta. Har ma suna yin musu da kuma jayayya suna cewa. ''ai wannan falalah da rahamar, ai ba Manzon Allah ake nufi ba'' - wal iyadhu billah.Saboda haka aganinsu, wai ba zamu yi murnar ba.. Ko kuwa sun manta da ayar nanne ta cikin suratul Anbiya : ''bamu aikoka ba, sai domin ka zama RAHAMA ga dukkan talikai'' (21:107)To bari mu duba muga MEYE MALUMAN TAFSIRI SUKA FA'DA AKAN WANNAN AYAR??1. Ibnul Jauziy (bataimiye ne, masanin hadisi, kuma marubucin litattafa da dama) ya fada dangane da ma'anar FALALAR ALLAH da RAHAMARSA cewar :''Dhahhak ya ruwaito daga IBN ABBAS (r.a) cewar -Falalar Allah tana nufin ILIMI (Kamar na Alqur'ani da Tauheedi).-ma'anar RAHAMAR ALLAH kuma, shine ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w).(aduba littafinsa mai suna 'Zadul masir fiy ilmit tafsir' -juzu'i na 4 shafi na 40).2.> Abu Hayyan Al-Andalusiy (r.a) shima ya fadi cewar ''FALALAR ALLAH tana nufin ILIMI. RAHAMAR ALLAH kuma tana nufin ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w).(aduba tafsirinsa mai suna 'BAHRUL MUHEET'juzu'i na 5 shafi na 171).3. AL IMAM JALALUD-DEEN AS-SUYUTY (r.a) yace ''Abush-Shaikh ya ruwaito daga Ibnu Abbas (r.a) yana cewa: 'ma'anar falalar Allah ita ce Ilimi.. Rahamar Allah kuwa, tana nufin Annabi Muhammadu (s.a.w.w) tunda Allah yace 'wama Arsalnaaka illaa RAHMATAN lil'alameen'.(aduba littafinsa Ad-Durrul Manthuur, juzu'i na 4, Shafi na 330).4. AL-'ALLAMATUL ALUSIY (r.h) shi cewa ma yayi 'ITA KANTA FALALAR MA AI ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w) take nufi''Yace ''Imamul Khateeb da kuma Ibn 'Asaakira sun ruwaito daga Ibnu Abbas (r.a) cewar - ma'anar falalar Allah, shine Annabi Muhammadu (s.a.w.w).(aduba littafin tafsirinsa mai suna 'Ruhul-Ma'aniy, juzu'i na 11 shafi na 141).Wadannan hamshaqan Malamai sun tabbatar mana da cewar wannan ayah ta cikin suratu Yunus (a.s) -ayah ta 58. Tana nufin ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w) shine falalar Allah, kuma shine rahamar Allah. Kuma saboda samuwarsa ne ya kamata muyi murna mu nuna farin cikinmu, ba wai domin samun wani abun duniya ba.Sai dai kash! Su wadannan masu juyayyen ra'ayi dangane da Murnar Samuwar Manzon Allah (saww); Zaka gansu ako yaushe sukan halarci bukukkunan Murnar haihuwar wasu masu kudin ko masu mulkin harma kaji su suna Jawabai awuraren taron.Kamar yadda Kwanakin baya suka halarci Birthday na wani Babban Mutum Akasar nan. Har ma wani mai jan-baqinsu yayi ta Karatun Alqur'ani awajen.Sannan Sukan fito suyi Murnar cikar wata makarantarsu ko Qungiyarsu wasu Shekaru.. (Kamar yadda kusan duk shekara sukan yi)Sannan ita ma Qasar Sa'udiyyah da take goyawa wannan Mummunan Ra'ayi baya, To ai SUNA YIN MAULIDIN IBN SA'UD (KAKANSU WANDA YA KAFA DAULAR). Sannan KUMA SUNA YIN MAULIDIN IBN ABDILWAHAB Duk shekara.Muhimmiyar tambayar da Zamu so su bamu amsar ta anan ita ce:* SHIN WADANNAN MAULIDAN NAKU DA KUKE YI MENENE MATSAYINSU ACIKIN ADDINI ???* SANNAN MENENE MATSAYIN BIKIN RANAR INDIPENDENCE DA GWAMNATIN QASAR NAN DA TA SA'UDIYYAH SUKE YI DUK SHEKARA ?* SANNAN MENENE MATSAYIN BIKIN NAN WANDA KU KAYI AKADUNA ASHEKARAR 2010 DOMIN TUNAWA DA WANI MALAMINKU WANDA YA MUTU??* SHIN WADANNAN AIYUKAN ADDINI YACE AYI SU?? KO KUWA KUNE KUKA YI RA'AYI KUKA QIRQIRA?* IDAN KU NE KUKA QIRQIRO SU, TO YAYA SUNANKU? KUMA YAYA SUNAN ABINDA KUKEYI?* IDAN KUMA ADDINI YA BAKU DAMAR KU YISU, TO A WANNE WAJE?* TA YAYA YIN WADANNAN TARURRUKAN YA ZAMA HALAL AMMA TARON MURNAN HAIHUWAR MANZON ALLAH (SAWW) SHI KUMA YA ZAMTO HARAMUN ??* IDAN KU KACE "AI SAHABBAI BA SUYI MAULIDI BA, AN FISU SON ANNABI NE?? MU KUMA SAI MUCE MUKU AI KUMA BASU TA'BA YIN TARON BUDE MASALLACI BA; BASU TABA YIN MUSABAQAH BA... shin an fisu son addini ne ???Amma in dai mutum hujjah yake nema Akan Maulidi ba wani abu daban ba, to ina ganin wannan ayar ta ishe shi.. Tunda dai ba hadith bane, ballantana ace bai inganta ba..Hanyar Zaman lafiya atsakanin Musulmi ita ce:* afidda son rai da bin son zuciya.* a tsaya abisa karantarwar Alqur'ani da Sunnar Annabi (saww) a aikace ba wai abaki ba.* Sannan alura da Ijma'in Malamai na addini. Na da dana yanzu.* in dai mutum yana hujjarsa ingantacciya ta yin abu abisa fahimtarsa daga Alqur'ani da hadisan Manzon Allah (saww); to bai kamata ayi masa inkari; ko harma arika kafirta shi ba.* Ba zai yiwu ya kasance iya fahimtarka ko fahimtar Malaminka ita ce kadai daidai acikin addini ba.. Saboda tun zamanin Sahabbai da Tabi'ai akan samu bambancin ra'ayi ko bambancin fahimta atsakaninsu. Amma ba sa kafirta juna kuma ba sa Bidi'antar da juna.Da fatan Allah ya Qara mana ilimi mai amfani. Kuma ya bamu wadatar zuci data fili, domin muyita hidima ga MASOYIN MU (s.a.w.w). Ya Allah ka Qara mana son NAJLUL HASHIMI (s.a.w.w).