Friday 2 May 2014

Part 2

Abinda zamu fara kafa hujja dashi, shine ayoyin Alqur'ani Mai Girma.Ayah ta farko za'a sameta acikin Suratu Yunus (a.s) surah ta 10 ya ta 58, Wajen da Allah (SWT) yake cewa: ''(YA MUHAMMADU) kace musu -da falalar Allah ne da kuma rahamarsa. Da wannan ya kamata suyi farinciki.. Domin shine mafi alkhairi daga (arzikin) da suke tarawa''.Toh gashi dai ayah tayi bayani Qarara, sai dai kash! Wadansu mutanen sun kasa fahimta. Har ma suna yin musu da kuma jayayya suna cewa. ''ai wannan falalah da rahamar, ai ba Manzon Allah ake nufi ba'' - wal iyadhu billah.Saboda haka aganinsu, wai ba zamu yi murnar ba.. Ko kuwa sun manta da ayar nanne ta cikin suratul Anbiya : ''bamu aikoka ba, sai domin ka zama RAHAMA ga dukkan talikai'' (21:107)To bari mu duba muga MEYE MALUMAN TAFSIRI SUKA FA'DA AKAN WANNAN AYAR??1. Ibnul Jauziy (bataimiye ne, masanin hadisi, kuma marubucin litattafa da dama) ya fada dangane da ma'anar FALALAR ALLAH da RAHAMARSA cewar :''Dhahhak ya ruwaito daga IBN ABBAS (r.a) cewar -Falalar Allah tana nufin ILIMI (Kamar na Alqur'ani da Tauheedi).-ma'anar RAHAMAR ALLAH kuma, shine ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w).(aduba littafinsa mai suna 'Zadul masir fiy ilmit tafsir' -juzu'i na 4 shafi na 40).2.> Abu Hayyan Al-Andalusiy (r.a) shima ya fadi cewar ''FALALAR ALLAH tana nufin ILIMI. RAHAMAR ALLAH kuma tana nufin ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w).(aduba tafsirinsa mai suna 'BAHRUL MUHEET'juzu'i na 5 shafi na 171).3. AL IMAM JALALUD-DEEN AS-SUYUTY (r.a) yace ''Abush-Shaikh ya ruwaito daga Ibnu Abbas (r.a) yana cewa: 'ma'anar falalar Allah ita ce Ilimi.. Rahamar Allah kuwa, tana nufin Annabi Muhammadu (s.a.w.w) tunda Allah yace 'wama Arsalnaaka illaa RAHMATAN lil'alameen'.(aduba littafinsa Ad-Durrul Manthuur, juzu'i na 4, Shafi na 330).4. AL-'ALLAMATUL ALUSIY (r.h) shi cewa ma yayi 'ITA KANTA FALALAR MA AI ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w) take nufi''Yace ''Imamul Khateeb da kuma Ibn 'Asaakira sun ruwaito daga Ibnu Abbas (r.a) cewar - ma'anar falalar Allah, shine Annabi Muhammadu (s.a.w.w).(aduba littafin tafsirinsa mai suna 'Ruhul-Ma'aniy, juzu'i na 11 shafi na 141).Wadannan hamshaqan Malamai sun tabbatar mana da cewar wannan ayah ta cikin suratu Yunus (a.s) -ayah ta 58. Tana nufin ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w) shine falalar Allah, kuma shine rahamar Allah. Kuma saboda samuwarsa ne ya kamata muyi murna mu nuna farin cikinmu, ba wai domin samun wani abun duniya ba.Sai dai kash! Su wadannan masu juyayyen ra'ayi dangane da Murnar Samuwar Manzon Allah (saww); Zaka gansu ako yaushe sukan halarci bukukkunan Murnar haihuwar wasu masu kudin ko masu mulkin harma kaji su suna Jawabai awuraren taron.Kamar yadda Kwanakin baya suka halarci Birthday na wani Babban Mutum Akasar nan. Har ma wani mai jan-baqinsu yayi ta Karatun Alqur'ani awajen.Sannan Sukan fito suyi Murnar cikar wata makarantarsu ko Qungiyarsu wasu Shekaru.. (Kamar yadda kusan duk shekara sukan yi)Sannan ita ma Qasar Sa'udiyyah da take goyawa wannan Mummunan Ra'ayi baya, To ai SUNA YIN MAULIDIN IBN SA'UD (KAKANSU WANDA YA KAFA DAULAR). Sannan KUMA SUNA YIN MAULIDIN IBN ABDILWAHAB Duk shekara.Muhimmiyar tambayar da Zamu so su bamu amsar ta anan ita ce:* SHIN WADANNAN MAULIDAN NAKU DA KUKE YI MENENE MATSAYINSU ACIKIN ADDINI ???* SANNAN MENENE MATSAYIN BIKIN RANAR INDIPENDENCE DA GWAMNATIN QASAR NAN DA TA SA'UDIYYAH SUKE YI DUK SHEKARA ?* SANNAN MENENE MATSAYIN BIKIN NAN WANDA KU KAYI AKADUNA ASHEKARAR 2010 DOMIN TUNAWA DA WANI MALAMINKU WANDA YA MUTU??* SHIN WADANNAN AIYUKAN ADDINI YACE AYI SU?? KO KUWA KUNE KUKA YI RA'AYI KUKA QIRQIRA?* IDAN KU NE KUKA QIRQIRO SU, TO YAYA SUNANKU? KUMA YAYA SUNAN ABINDA KUKEYI?* IDAN KUMA ADDINI YA BAKU DAMAR KU YISU, TO A WANNE WAJE?* TA YAYA YIN WADANNAN TARURRUKAN YA ZAMA HALAL AMMA TARON MURNAN HAIHUWAR MANZON ALLAH (SAWW) SHI KUMA YA ZAMTO HARAMUN ??* IDAN KU KACE "AI SAHABBAI BA SUYI MAULIDI BA, AN FISU SON ANNABI NE?? MU KUMA SAI MUCE MUKU AI KUMA BASU TA'BA YIN TARON BUDE MASALLACI BA; BASU TABA YIN MUSABAQAH BA... shin an fisu son addini ne ???Amma in dai mutum hujjah yake nema Akan Maulidi ba wani abu daban ba, to ina ganin wannan ayar ta ishe shi.. Tunda dai ba hadith bane, ballantana ace bai inganta ba..Hanyar Zaman lafiya atsakanin Musulmi ita ce:* afidda son rai da bin son zuciya.* a tsaya abisa karantarwar Alqur'ani da Sunnar Annabi (saww) a aikace ba wai abaki ba.* Sannan alura da Ijma'in Malamai na addini. Na da dana yanzu.* in dai mutum yana hujjarsa ingantacciya ta yin abu abisa fahimtarsa daga Alqur'ani da hadisan Manzon Allah (saww); to bai kamata ayi masa inkari; ko harma arika kafirta shi ba.* Ba zai yiwu ya kasance iya fahimtarka ko fahimtar Malaminka ita ce kadai daidai acikin addini ba.. Saboda tun zamanin Sahabbai da Tabi'ai akan samu bambancin ra'ayi ko bambancin fahimta atsakaninsu. Amma ba sa kafirta juna kuma ba sa Bidi'antar da juna.Da fatan Allah ya Qara mana ilimi mai amfani. Kuma ya bamu wadatar zuci data fili, domin muyita hidima ga MASOYIN MU (s.a.w.w). Ya Allah ka Qara mana son NAJLUL HASHIMI (s.a.w.w).

1 comment:

  1. Allah sarki qaramin tunanin ku bazai taba sawa nake kula aiyukan ku ba saboda naja baya dan sainama wankin babban bargo kaida mallaman naka

    ReplyDelete