Friday 2 May 2014

Part 1

BismilLahir Rahmanir Raheem.***************************Tsira da amincin Allah su tabbata ga Hasken Hasaka, Annabinmu masoyinmu Muhammadu (s.a.w.w) da iyalan gidansa da dukkan sahabbansa.. Ameen.TARON MAULUDI dai wani taro ne wanda ake yinsa domin Tunawa da Kuma Murnar haihuwar Manzon Allah (saww).Jama'ar Musulmi sukan taru waje daya ne suyi Walimah, Sannan Su tunatar da Junansu dangane da wasu muhimman lamura acikin rayuwar Manzon Allah (saww).Kamar tarihin rayuwarsa tun daga haihuwarsa, da kuma Muhimman Al'amuran mamaki da suka faru alokacin haihuwar tasa (saww). Da kuma labarin Hijirarsa, da yake-yakensa da irin gwagwarmayar da yasha fama da ita alokacin isar da aiken Ubangijinsa (swt).Bayan haka akan tabo labarin Mu'ujizozinsa da Khasa'isu nasa (saww).Sannan Masu taron Sukan yi wasu ayyuka na Ibada awajen kamar Wa'azantar da juna da Karatun Alqur'ani Mai Girma; da Zikiri da Salatin Annabi (saww). sannan kuma sukan Sadar da Zumuncin Junansu.Wannan yasa dukkan musulmin kirki suke murna dashi, domin kuwa taro ne wanda ake yinsa domin nuna murna da kuma godiyarmu ga Ubangiji Allah abisa baiwar da yayi mana ta samun fiyayyen Halitta (s.a.w.w.) wanda shi ya fitar da duniya daga duhun jahilci da kafirci, izuwa hasken ilimi da Imani.. Saboda haka babu wanda yake baQin-ciki ko bacin rai dangane da harkar Mauludi sai shaitan da'yan uwansa..Kamar yadda Ibn Katheer ya kawo acikin littafinsa 'ALBIDAYAH WAN-NIHAYAH'_ cewar: ''Shaitan Iblis yayi kuka yayi kururuwa ne har sau hudu alokuta daban-daban.. 1. Lokacin da aka la'anceshi, 2. Da lokacin da aka jefoshi nan duniya. 3. LOKACIN DA AKA HAIFI ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w) 4 lokacin da aka saukar da surar Fatiha.. (aduba juzu'ina 2, shafi na 166).Mu kuwa Muminai Masoyansa (s.a.w.w) muna taruwa muna yin murna ne saboda bin umurnin Allah (s.w.t) a inda ya umurce mu cewar muyi farin ciki da samun falalarsa da Rahamarsa..''DA FALALAR ALLAH ne da Kuma RAHAMARSA, da wannan (ya kamata) suyi farin-ciki, domin shine mafi alkhairi daga abinda suke tarawa (kamar dukiya, dss)''INSHA ALLAH zan kawo hujjoji kamar haka:1. ayoyi daga Alqur'ani mai girma tare da irin fassarar da Manyan Maluman Musulunci masanan Tafsiri suka yiwa Ayoyin.2. Hadisai ingattattu wadanda suke nuna ishara izuwa wannan Muhimmin lamari.3. Maganganun Manyan Maluma Mufassarai da fuqaha'u.4. Ijma'in malamai na maz-habobi.Da fatan Allah ya tabbatar da zukatanmu abisa Qaunar Masoyinmu (s.a.w.w)

No comments:

Post a Comment