Friday 2 May 2014

Part 5

ALHAMDULILLAHI mun gode ma Allah wanda ya sanya mu acikin kebantattun wannan al'ummah wajen nuna murnarmu da biyayya da girmamawa abisa Janibin SHUGABA (s.a.w.w).Awancan sati da ya gabata, na kawo wasu daga cikin ayoyin Alqur'ani mai girma wadanda suke ishara izuwa halascin yin taro domin murna da farin-ciki da samun Manzon Allah (S.A.W.W). Kuma na kawo fassarorin da Manyan malamai masanan tafsiri suka yima ayoyin.Kamar yadda Shaikh Muhammadul Alawiy Almalikiy yake cewa ''mu ba wai muna magana ne akan halascin yin mauludi sau daya, ko wata daya ashekara kawai ba, A'A. mu muna magana ne tare da kafa hujjoji akan WAJIBCIN tuna shi da kuma yin mauludinsa ako yaushe ako wacce rana''.''Sai dai dole ne ya zamto murnar mu da karsashin mu ta fi yawaita acikin watan Rabi'ul Awwal, domin shine watan da aka haifa mana wannan BABBAN MASOYI (s.a.w.w)'Yan uwa ku sani cewar yin murna da girmama wata rana ko wani lokaci kebantacce saboda dalilin wata kebantacciyar baiwa wacce Allah yayi maka, wannan ba bid'ah bane. Ba kuma sabon abu bane acikin addini.Domin kuwa yazo acikin Sahihul Bukhariy da Sahihu Muslim a Kitabul fadha'il, da kitabu salatil jumu'ah, da kitabur- riqaaq, wajen da Manzon Allah(s.a.w.w) yake fadar falalar ranar Jumu'ah. Yana cewa ''acikinta ne aka halicci Annabi Adam, kuma acikinta ne aka karbe rayinsa..''Kunga kenan ashe wannan yana daga cikin dalilan da yasa ranar jumu'a ta zama ranar Eedi ga Musulman wannan Al'ummah..Kuma an ruwaito cewar Shi kansa (s.a.w.w.) ya kasance yana girmama RANAR DA AKA HAIFE SHI.Domin kuwa Abu-Qatadah Al-ansariy (r.a) ya ruwaito cewar an tambayi SHUGABA (s.a.w.w) dangane da azumin da yake yi duk ranar litinin. Sai yace:''ita ce RANAR DA AKA HAIFENI, kuma ita ce ranar da aka fara saukar min da wahayi''(aduba Sahihu Muslim, hadith mai lamba 2606, da kuma SUNANUL KUBRA na Imamul Baihaqiy, juzu'i na 4, shafi na 300, hadith mai lamba 8182, Da kuma mai lamba 8259.. Imamu Ahmad, da Imam An-Nasa'i duka sun ruwaito kuma sun inganta hadithin)Ga hujjah nan ta bayyana Qarara cewar Manzon Allah (s.a.w.w) yana yin azumin ne domin nuna godiyarsa ga Allah (SWT) abisa ni'imar bayyanar dashi aduniya, da kuma ni'imar sanya shi acikin Manzanni (a.s.). Shi yasa yake yin wannan ibadah ta Musamman.To saboda haka ya halasta mutum yayi ado, ya tara jama'a, ya chiyar ya shayar domin MURNA da kuma GODIYA ga Allah (swt) abisa ni'ima da baiwar da yayi mana da ya bamu MANZON ALLAH (s.a.w.w). saboda shima ciyarwar da shayarwar, duk fannin ibada ne..Saboda haka duk mai cewa 'ai Annabi be yi Maulidi ba' to Qarya ne.. Annabi yayi.. Domin kuma ba wani abu bane maulidin illa nuna murna da kuma godiya ga Allah abisa wata ni'imar da yayi..Saboda Maluman Usulul-Fiqhi sunce ana cirowa Hukunci ne ta hanyoyi biyar kamar haka:1. ZAHIRIN NASSI.2. ISHARA DAGA NASSI.3. DILALAR DA NASSIN YA SHIRYAR.4. ABINDA NASSIN BA YA CIKA SAI DASHI.5. KO KUMA MAFHUMUL-MUKHALAFAH.Masu Qin Mauludi suna tambaya ta cewar ''toh munji ka kafa hujja da dalilai masu Qarfi akan halarcin taruwa ayi Maulidi. To me yasa sahabbai basu yi ba?''Na baku amsa a (part 3) amma naga kamar har yanzu baku gamsu ba, to ku jira fitowar (part 6) INSHA ALLAHU Zan ci gaba daga inda na tsaya.Ya Rasullahi ka yarda da soyayyar da muke yi maka don albarkacin Nana Fatimah (a.s.) ameen.

No comments:

Post a Comment