Friday 2 May 2014

Part 7

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin da ya Qagi halittar sammai da Qassai, sannan ya sanya duhu da haske acikinsu.Tsira da Aminci da Karimci da daraja su Qaru, su wanzu har abada abisa BABBAN BAWAN ALLAH, RAHAMAR ALLAH, FALALAR ALLAH, ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w) Da iyalan gidansa tsarkaka, da Sahabbansa madaukaka..Izuwa yanzu na tabbata duk mutumin da zuciyarsa take cike da imani ya gamsu da dukkanin hujjojin da muka yi magana akansu tun daga kashi na farko acikin wannan tattaunawa har izuwa kashi na 6.To amma duk da haka sai naga cewar ya kamata in sake kawowa ko da aya daya ne daga cikin Alqur'ani mai girma da kuma hadisi don Qarfafa dalili, kafin kuma in ci gaba da lissafa sunayen wasu daga Manyan Malaman duniya wadanda suka tafi akan wannan kyakkyawar fahimta ta yin taron maulidi domin girmama Annabi (s.a.w.w.).Acikin suratu Hud (a.s.) bayan Allah (s.w.t) ya gaya ma Manzonsa (s.a.w.w) labarurrukan Annabawan da suka gabace shi da kuma irin gwagwarmayar da sukayi da al-ummominsu, daga Qarshen surar sai yace masa:''kuma da yawa mukan Qissanta maka daga labarurrukan Manzanni (wadanda suka gabata). Gwargwadon yadda zamu tabbatar (zamu Qarfafa ) maka zuciyarka''. (sur. Hud, 119).Shehu Ibrahim Niasse (r.a) yake cewa ''in dai har Manzon Allah (s.a.w.w) zuciyarsa zata Qarfafa idan an bashi labarin Annabawan da suka gabata, to yaya kuma mu namu zuciyoyin ba zasu Qarfafa ba idan an karanta mana tarihin Manzon Allah (s.a.w.w).. (au kama Qalash Shaikh).To jama'a idan muka kalli wannan ayah da idon basira, ai ita kadai ma ta ishe mu hujjar taruwa ayi Maulidi.Jama'a Maulidin nan fa wallahi ayyukan alkhairi ne masu dimbin yawa akunshe acikinsa. Misali:a.) wa'azi da tunatarwa da nasihohi ta hanya jiyar da al-ummah tarihin Manzo (s.a.w.w) da yakokinsa da sauran gwagwarmayar da yasha fama da ita domin isar da saqon Ubangiji (S.W.T).b.) Karatun Alqur'ani da hadisan Manzo (s.a.w.w).c.) Rera yabon Manzon Allah (s.a.w.w) da iyalan gidansa Sahabbansa wadanda suka taimakeshi wajen isar da sakon Ubangiji (s.w.t.).d.) zikirin Allah da salati ga SHUGABA (s.a.w.w).e.) shigar da soyayyarsa da Qaunarsa cikin zukatan manya da Qanqana, ta hanyar fa'dar siffofinsa da halayensa, da mu'ujizozinsa (s.a.w.w).f.) taimakawa juna cikin bin Allah, ta hanyar zumunci da kuma haduwa da juna abisa manufa guda. Wato girmama Manzon Allah (s.a.w.w).g.) ciyarwa da shayarwa fi-sabilillahi.To 'Yan uwa idan kuka dubi wadannan abubuwan da na lissafta a sama da ma wasunsu wadanda na manta ban fa'da ba, ai zaku ga cewar dukanninsu ayyukan alkhairi ne wadanda musulunci yake umurni dasu.Da wannan nake Qara ba ma 'Yan uwana shawarar cewa lallai ne mu kawar da kanmu daga maganganun maqiya, kuma muci gaba da girmama Manzon Allah (s.a.w.w) da kuma duk wani mutum ko wani abu wanda yake da nasaba dashi (s.a.w.w).Domin kuwa Manzo (s.a.w.w) ya bamu labarin cewar adaren da akayi Isra'i da Mi'iraji da shi, lokacin da suka iso wani gari wato ''Baitul laham'' (bethlehem) sai Mala'ika Jibrilu (a.s) ya umurce shi da cewar ya sauko yayi sallah raka'a biyu.Bayan ya idar sai Mala'ikan ya tambayeshi ''YA MUHAMMADU ka san ko awanne waje ne kayi sallah?''Sai yace masa ''A'a''Sai yace ''ai kayi sallah ne awajen da aka haifi Annabi Eesa (a.s).To anan zamu iya fahimtar cewa ashe guraren da aka haifi Annabawa (a.s) suna daga cikin 'Sha'a'irul Lah'.(alamomi, ko kuma guraren girmamawa na Allah). Ba don haka ba, da Mala'ika Jibreelu (as) ba zai umurci Manzon Allah (saww) cewar yayi sallah awajen ba.* In dai har guraren da aka haifi Annabawa yana da muhimmanci acikin addini, to yaya kuma RANAKUN HAIHUWAR, DA KUMA WADANDA SUKA HAIFESUN??Don karin bayani Aduba sunanun Nasa'i, juzu'i na 1, shafi na 241, hadith mai lamba 448).Ya Allah ka Qara cika zuciyoyinmu da tsantsar Qaunar Manzon Allah (s.a.w.w) da kuma Girmama shi tare da dukkan abinda ya rataya dashi.Masu tada jijiyar wuya, suna kumfar baki har suna Kafirta Muminai Masoyan Manzon Allah (saww) saboda suna yin Maulidi, ko kuma awasu lokutan sai kaji suna kiran mutane da sunannaki Kala-Kala.Ko suce maka Dan-bidi'ah, Ko suce maka mushriki, duk dai saboda kana Girmama Manzon Allah (saww) ta hanyar da su ba'a koyar dasu ba.Ko ba'a yiwa mutum bayani ba, yasan cewar Wadannan kalmomin da makamantansu, basu acikin koyarwar Islama.Shi taron Maulidi mu mun dauke shi amatsayin wata sunnah ce mai kyau daga cikin sunnonin Musulunci.Domin kuwa tun farkon musulunci akwai irin wadannan ayyukan. Kuma Manzon Allah (saww) yana cewa:"DUK WANDA YA SUNNANTA WATA SUNNAH MAI KYAU ACIKIN MUSULUNCI, TO YANA DA LADANTA DA KUMA KWATANKWACIN LADAN WADANDA SUKAYI AIKI DA ITA. BA ZA'A TAUYE KOMAI DAGA LADANSU BA. HAR ZUWA TASHIN ALQIYAMAH. KUMA DUK WANDA YA SUNNANTA WATA MUMMUNAR SUNNAH ACIKIN MUSULUNCI, TO YANA DA ZUNUBINTA DA KUMA KWATANKWACIN ZUNUBIN DUK WANDA YAYI AIKI DA ITA HAR IZUWA TASHIN ALQIYAMAH.BA ZA'A TAUYE KOMAI BA DAGA CIKIN ZUNUBINSU"(aduba Sahihu Muslim, hadisi na 1017).Idan muka dubi irin kyawawan ayyukan da suke kunshe acikin wannan al'amarin na TARON MAULIDI, mu da kanmu mun san cewar Taron Maulidi yana daga cikin "SUNNATUN HASANATUN" din da ake nufi.Sannan adaya gefen idan muka dubi muka dubi yadda wasu suke kafirta 'yan uwansu musulmi tare da zaginsu da bakaken maganganu, don kawai sabanin fahimta, da kuma yadda suke raba kan al'ummar Annabi (saww) tabbas ko shakkah babu mun san inda zamu ajiye su shine.. "SUNNATAN SAYYI'ATAN".Da fatan Allah ya kiyaye mana imaninmu.Insha Allahu akashi na takwas zan kawo mana misalai daga cikin ayyukan magabata.

1 comment: