Friday 2 May 2014

Part 4

A ci-gaba da Muke yi wajen Tsamowa Nassosi daga Ayoyin Al-Qur'ani mai girma wadanda suke yin ishara izuwa Halarcin taruwa ayi Murna da Zuwan Annabin Rahama (saww), Wannan Karon muna so 'yan uwa suyi duba da idon basira izuwa wasu ayoyi guda biyu masu kama da juna wadanda kuma dalilin saukarsu ya zamto kusan iri daya.Wannan Ayar tazo ne afarko-farkon Suratul-Jumu'ah, Bayan Allah (swt) Ya gayawa Muminai ni'imar da yayi musu ta dalilin Aikowar Annabi (saww), sai kuma yace:''Wannan falalar Allah ce, yana bayar dashi ga wanda yaso. Kuma Allah Ma'abocin falalah mai girma ne'' - (Suratul Jumu'ah Aya ta 4; da kuma suratul hadeed aya ta 28)Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (r.t.a) ya fassara wannan aya ta sama da cewa:Ma'anar ''Allah ma'abocin falala mai girma ne'' shine saboda MUSULUNCI da kuma ANNABTAR da ya bayar ga ANNABI MUHAMMAD (s.a.w.w.).Awani Qaulin kuma aka ce ma'anar 'Falala mai girma' ita ce musulunci.Awani Qaulin kuma aka ce 'MANZON ALLAH (s.a.w.w) da kuma ALQUR'ANI MAI GIRMA, sune wannan falala da ake nufi.(aduba ''TANWEERUL MIQBAAS MIN TAFSEERI IBN ABBAAS don Qarin bayani)To 'yan uwa, abin lura acikin fassarar wannan aya shine: ita ma tana tabbatar mana da cewa ANNABINMU (s.a.w.w) shine FADHLUL-LAHI (falalar Allah)..To ashe shi ake nufi da cewar MUYI MURNA saboda shi.. (acikin ayar 58 ta suratu Yunus a.s).Idan kuma mutum ya dage akan cewar "FADHLUL-LAHI" tana nufin Musulunci ne ko kuma Alqur'ani Mai girma, ba Annabi (saww) ba, To Sai mu tambaye shi:TA DALILIN WANENE AKA SAMU MUSULUNCIN DA KUMA AL-QUR'ANIN???Amsar dai guda daya ce- "MAULANA MUHAMMADUR-RASULULLAH (SAWW)"* Hujjah ta tagaba tana cikin suratu Maryam (a.s), dangane da tarihin Annabi Yahya (a.s). Allah (s.w.t) yana ce mana: ''KUMA AMINCIN ALLAH YA TABBATA AGARESHI ARANAR HAIHUWARSA, DA RANAR MUTUWARSA DA KUMA RANAR DA ZA'A TASHESHI YANA RAYAYYE'' (sur. 19, aya ta 15).Wannan ayar tana ishara agaremu cewar RANAR HAIHUWAR ANNABAWA (a.s.) ashe RANAR AMINCI CE ga shi kansa Annabin da kuma al'ummar da aka aikoshi cikinsu..Kuma Allah bai hana muyi murna da muhimman ranaiku acikin rayuwarmu da addininmu ba.Awani Wajen Kuma Allah (s.w.t) yake cewa: ''Hakika mun aiki Annabi Musa da ayoyinmu (da kuma umurnin) cewar ''Ka fitar da mutanenka daga duhun (kafirci) izuwa haske.. Kuma ka tunasar dasu Dangane da RANAKUN ALLAH'' (aĆ½yamil Lah)- suratu Ibraheem (a.s) sur. 14 aya ta 5.* Menene Ma'anar kalmar 'RANAKU ko kuma KWANUKAN ALLAH'??Al-Imamul Baihaqiy ya ruwaito acikin littafinsa 'SHU'ABUL IMAN' cewar: "Ma'anar KWANUKAN ALLAH shine albarkokinsa da kuma ayoyinsa.To idan kuwa haka ne, to wacce FALALA CE, wacce NI'IMA CE, wacce ALBARKA CE ta kai kamar samun ANNABI MUHAMMADU (s.a.w.w)???Don Allah Ku bani amsa.

No comments:

Post a Comment