Friday 2 May 2014

Part 6

Tsira da Amincin Allah da daukaka da daraja da martaba su Qara tabbata ga MATATTARAR BAIWA, ALFAHARIN BANU HASHIM, ANNABI MUHAMMADU da iyalan gidansa tsarkaka da sahabbansa mahaskaka..Bayan haka ina Qara jawo hankalin duk wani masoyin Annabi (s.a.w.w) da cewar Mu dage mu jajirce muyita hidima domin nuna murnar mu dangane da tunawa da haihuwar FIYAYYEN MANZANNI (s.a.w.w).Domin kuwa yin haka ibadah ce wacce take matukar Qara kusantar da bawa izuwa rahamar Mahaliccinsa. Kuma ana amfana da ita: Ko da kuwa wanda ba Musulmi ba idan yayi murna da zuwan Annabi Muhammadu (saww) to Wallahi zai amfana.Imamul Bukhariy ya ruwaito hadisi daga 'Urwatu (r.t.a) cewa: ''Thuwaibah baiwar Abu-lahab ce wacce ya 'Yanta ta (saboda murna alokacin da ta bashi labarin haihuwar Annabi s.a.w.w) sannan kuma daga baya ta shayar da Manzon Allah (s.a.w.w).Bayan Abu-lahab ya mutu, sai wani (Sahabi mumini) daga cikin danginsa ya ganshi amafarki acikin mummunan yanayi. Sai ya tambaye shi.. ''Ya aba_lahab, me ka riska?''Sai yace ''Wallahi tunda na rabu daku ban samu wani hutu ba. Sai dai kawai ana shayar dani ruwa (mai dadi) ta tsakanin babban yatsana da sauran yatsu, saboda dalilin 'Yantar da Tsuwaibah da nayi''(aduba Sahihul Bukhariy Juzu'i na 7, hadisi na 38 acikin Kitabun-nikahi).To Jama'a wannan fa kafiri ne, kuma babban makiyin Annabi (s.a.w.w) amma gashi ya amfana ta dalilin yayi murna da haihuwa Annabi (s.a.w.w).. To yaya kuma Musulmi Mumini sadiqi idan ya tara jama'a ya ciyar dasu ya shayar dasu don nuna Qauna da murnarsa saboda zuwan Manzon Rahama (s.a.w.w)!!Kuma Karku manta cewar shi fa Abu-Lahab alokacin da ya nuna wannan murnar, yayi ne domin zumunci. Ba wai don girmama Annabin ba.Domin kuwa alokacin bai san WANNAN JARIRIN SHINE ANNABIN QARSHE BA, BAI SAN CEWAR WANNAN JARIRIN SHINE MAFI DARAJAR HALITTAR ALLAH BA. (saww).Kuma ku dubi irin amfanuwar da ya samu ta dalilin wannan murnar da yayi sau daya.. Duk da cewar daga baya ya zamto Qaton kafiri, mafi chutarwa ga Annabi (saww).Sannan wata isharar da zamu sake daukowa akan Halaccin Taron Maulidi daga Hadisan Annabi (saww) shine: A lokacin da SHUGABA (s.a.w.w.) yazo madina ya samu Yahudawa suna azumi tare da bukunkuna. Sai ya tambaya saboda menene?Sai aka ce masa ''SUNA YI NE SABODA TUNAWA DA RANAR DA ALLAH YA TSERATAR DA ANNABI MUSA (AS) DAGA SHARRIN FIR'AUNA"Sai Annabi (s.a.w.w) yace ''AI MU MUKA FISU CHANCHANTA DA ANNABI MUSA.''Saboda haka ya umurci musulmai suma su rika yi..(aduba Sahihu Muslim, juzu'i na 2, shafi na 147, hadithi mai lamba 1130).Abin lura acikin wannan hadisin shine:a.) Annabi (s.a.w.w) ya yarda da yin wata ibada ta musamman domin tunawa da wani abu muhimmi na tarihi.b.) Musulunci yana karbar abu mai kyau wanda babu sa'bon Allah acikinsa. Ko da kuwa daga gun yahudawa ne.c.) In dai har Annabi (s.a.w.w) ya yarda agirmama ranar da Allah ya tseratar da Banu Isra'eela daga zaluncin fir'auna, to ashe kenan muma ya kamata, ya kuma dache mu girmama ranar da Allah ya kawo mana RAHAMARSA wanda ya tseratar da DUKKAN duniya daga duhun kafirci da jahilci da zalunci.. wato Annabi Muhammadu (s.a.w.w).Na san zaku yimin tambayar da kuka saba yimin.. cewar to me yasa Sahabbai (r.t.a) su basuyi ba??To ni kuma sai in baku amsa daki-daki kamar haka:a.) kasancewar Annabi (s.a.w.w) be yi abu ba, Sahabbansa basuyi ba, BA HUJJAH BANE cewar na bayansu ba zasu yi ba.!!.Hujjah ita ce kace mana ANNABI YA HANA..Kamar yadda na fa'da a chan bayan (part 3),Ya kamata kusan cewar asalin kowanne abu halal ne acikin addini. Saidai kadai wanda shari'a ta hana. Ta hanyar aya ko hadith ingantacce..B.) Imamu Ahmad ya ruwaito hadithi daga Ibn Mas'udin cewar ''Duk abinda Musulmi suka hadu akan cewar yana da kyau, to agun Allah ma mai kyawu ne..''Kunga kuma duk musulmin duniya sun yarda da cewa MAULIDI ABU NE MAI KYAU.In banda wahabiyawa babu wani wanda yake jayayya akan wannan..Su ma muna yi musu fatan Allah ya ganar dasu..C.) duk wani abu mai kyawu wanda yake akwai wata maslaha ta addini acikinsa, to yinsa halal ne..Idan kuwa muka duba da idon basira zamu ga akwai Masalihu Masu yawa acikin Taron Maulidi wanda al'ummar Musulmi Suke yi ayau.Misali:1. Halartar guraren Maulidi yakan Qara wa Mutum Jin nauyi da kuma ganin girman Annabi (saww). Saboda Zurfafan Maganganu da zaka ji acikin tarihinsa (saww) wadanda idan littafi zaka Sanya agaban Malami, to sai kayi shekara da shekaru iliminka bai kai gun ba. Amma Idan ka halarci wajen Maulidi sai kaji ana ta fadarsu.2. Halartar wajen Maulidi yana Qara chusa wa Qananan Yaranmu Son Annabi (saww). Ta yadda zaka ji yaro Qanqani ya iya rera Qasidun Yabon Ma'aikin Allah (saww).Yin hakan kuwa ya dache da bin umurnin Annabi (saww) acikin Mash-hurin Hadisin nan: "ADDIBU AULADAKU"3. Halartar Guraren Maulidi yakan bada wata muhimmiyar dama ga Al'umar Musulmi domin sada zumuncin da yake tsakaninsu, da Kuma samun lada ta hanyar ciyarwa da shayarwa da kuma Wa'azantar da Juna.D. A Musulunci akwai abinda ake kira "AS-SUNNATUL-HASANAH". Maulidi yana daga cikin wannan jerin abubuwan

No comments:

Post a Comment